HausaZaɓen 2023: Hukumar INEC ta Ƙaddamar da Manhajar Intanet...

Zaɓen 2023: Hukumar INEC ta Ƙaddamar da Manhajar Intanet Domin Rajista

-

- Advertisment -spot_img

Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa wato Farfesa Mahmood Yakubu, a yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce hukumar ta ƙirƙiri manhajar ne domin masu zaɓe su fara rajista a duk inda suke ta kafar yanar gizo.

Ya ƙara da cewa ana buƙatar masu zaɓe da su tabbatar cewa sun shigar da bayanan su na ainihi a kafar ta yanar gizo kafin daga bisani a buƙaci su ziyarci rassan hukumar zaben domin kammala rajistar.

Yakubu ya ƙara da cewa hukumar zaɓe ta ƙirƙiri wannan manhajar ta yanar gizo ne saboda rashin tsaro da wasu sassa na Najeriya ke fama da shi. Hakan zai ba da dama ga ‘yan ƙasa su fara rajistar kafin hukumar zaɓe ta fara rajistar a ɗaukacin ƙasa baki ɗaya.

“Yin rajistar ta kafar yanar gizo zai bai wa masu zabe damar canja bayanai idan an yi kure ko kuma canja katin zaɓe in ya samu matsala da dai sauran abubuwan da mai zaɓe ke iya yi idan ya je ofishin hukumar zaɓe.

“Muna fatan wannan sabon ƙudurin zai rage cunkoso da ake samu a rassan rajistar zaɓe musamman ma a wannan lokaci na annobar Korona, sannan ya samar da sauƙin rajista ga ‘yan Najeria a fadin ƙasar.

“Haka ma yin wannan rajistar kyauta ne. Hukumar INEC ba ta da wasu ofisoshi da ta ƙayyade domin yin wannan rajista, ko kuɗin sayen kati ko kudin rajista. Kowa na iya yin wannan rajistar daga wayoyin hannu masu aiki da yanar gizo.” a cewar Farfesa Yakubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest news

Bawa Hale and Hearty After Slumping in Aso Rock – EFCC

The Chairman of the Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) Abdulrasheed Bawa slumped at the third National Identity Day...

Nigeria’s Cumulative Debt Hits N35.4tr

Nigeria’s total Public Debt Stock (PDS) has reached N35.465 trillion as of June 30 this year, the Debt Management...

Zamu Baiwa Jonathan Damar yin Takara idan yana so – APC

Uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta bayyana cewar idan har tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya tsallako cikin...

Bandits Kill One, Abduct Nine in Sokoto Village

Gunmen suspected to be Bandits believed to have escaped from the military onslaught in neighboring Zamfara State have killed...
- Advertisement -spot_imgspot_img

Hukumar Zakkah ta kaddamar da dashen-itacen dabino a Sakkwato

A lokacin bikin kaddamarwar, Mataimakin-Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Muhammad Maniru Dan'iya wanda shine ya wakilci Gwamnan jiha, Hon. Aminu...

West ham FLOP Haller nets Four goals in his Ajax UCL Debut

Sebastian Haller makes history as he scores four goals in Ajax 1 -5 trashing of Sporting CP in his...

Must read

STATEMENT: Sokoto is Home to Every Nigeria by Gov. Tambuwal

(Being text of the address Gov. Aminu Waziri Tambuwal...

Tambuwal’s Legacies: Business no More as Usual for Thieves in Sokoto State by Dr. Nasir Daniya

In the Seat of the Caliphate, gradually, both the...
- Advertisement -spot_imgspot_img

You might also likeRELATED
Recommended to you